HKI Ta ce Ta Tsaida Yaki A Gaza Na Wani Lokaci

Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sun tsaida yaki na wucin gadi a gaza, don baya kungiyoyin agaji na MDD su shigar da abinci

Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sun tsaida yaki na wucin gadi a gaza, don baya kungiyoyin agaji na MDD su shigar da abinci zuwa zirin gaza inda Falasdinawa suke mutuwa saboda yunwa.

Banda haka majiyar sojojin yahudawan ta bayyana cewa za’a fara jefawa Falasdinawan abinda daga sama daga kasar Jordan. Kamar yadda wasu kasashe turai suka yi alkawalin za’a yi.

Babu wata majiya ta MDD ko kuma na kungiyoyin agaji masu zaman kansu da suka tabbatar da labarin. Kuma mafi yawan kungiyayin sun bayyana cewa sai gani a kasa. Don hki ba abar amincewa bace. Tun shekara ta 2023 ne HKI ta kara tsananta hana shigo da abinci gaza. Kuma tun bayan fara yakin yahudawan sun kashe falassdinwa akalla 60000. sannan wasu fiye da dubu 130 sun ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted