An Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Yan MKO A Nan Iran

Ma’aikatar sharia a nan Tehran ta bada sanarwan yake hukuncin kisa kan mutane biyu mambobi a kungiyar yan ta’adda ta MKO ko wadanda aka fi

Ma’aikatar sharia a nan Tehran ta bada sanarwan yake hukuncin kisa kan mutane biyu mambobi a kungiyar yan ta’adda ta MKO ko wadanda aka fi sani da munafukai.

Kamfanin dillancin larabann Tasnim na JMI ya nakalto majiyar ma’aikatar na cewa mutanen biyu  Mahdi Hassani da Behrouz Ehsani, sun yi amfani da makamai wadanda suka hada da gurneti da kuma wasu ind suka kashe mutane fararin hula a dai dai lokacinda ake hargitsi a cikin kasar don tada hankalin mutane da kuma wargaza harkokin tsaro a cikin kasar.

Labarin ya kara da cewa an tabbatar Ba tare da wata shakka ba suna aiki tare da kungiyar ta MKO wadanda suke adawa da JMI tun ranar kafa ta.

Kungiyar MKO dai it ace babban kungiya wacce take adawa da JMI ta kuma kashe mata manya-manyan malaman addini a farkon nasarar juyinn juya halin musulunci a kasar. Sannan daga baya tare da taimakon gwamnatin kasar Iraki ta yaki JMI a warare da dama. Daga  karshe ta maida cibiyarta zuwa kasashen turai da Amurka inda suke samun makudan kudade don kimar da JMI. MKO ta kashe mutanen iran akalla 17000 tun lokacin shekara 1979 ya zuwa yanzu. an zartar da hukuncin a safiyar yau lahadi ,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted