Kungiyar yan tawaye M23 wacce take iko da yanki mai yawa a gabacin Democradiyyar Kongo ta bada sanarwan cewa idan gwamnatinn kasar Kongo bada gaggauta sakin fursinonin kungiyar ba, to tana iya kauracewa tattaunawan da za’a gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a watan mai zuwa.
Shafin yanar gizo na Africanews ya nakalto babban sakataren kungiyar kuma mai magana da yawunta yana fadar haka a ranar jumma’a.
Ya kuma kara da cewa bayan da kowa ya bayyana matsayinsa a wata mai zuwa ne ake saran bangarorin biyu wato gwamnatin kongo da kuma kungiyar M23 zasu rattaba hannu a kan yarjeniyar sulhu na gaskiya.
Ya ce tattaunawa da kuma amincewa da wasu ka’idoji wanda bangarorin biyu suka rattabawa hannu a watan da ya wuce a doha, sharer fage ne na yarjeniyar da za’a rattabawa hannu a ranar 18 ga watan Augusta mai zuwa a birnin Doha na kasar Qatar. Benjamin Mbonimpa ya jaddada cewa a cikin alkawalin da suka dauka a taron Doha na farko shi ne a saki fursinonin M23 kafin taro nag aba, don haka idan an ki yin haka tabbas ba zamu je taro na gabata.
A halinn yanzu dai kungiyar M23 suna iko da mafi yawan lardin kivu na gabacin kasar Kongo.