Hizbullah: Amurka Ta Sakewa HKI Linzamin Kan Tayi Abinda Ta Ga Dama A Lebanon

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi tir da hare-haren da HKI takai kan Wadi –Faraa a lardin Bikaa ta Arewa na kasar Lebanon inda

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi tir da hare-haren da HKI takai kan Wadi –Faraa a lardin Bikaa ta Arewa na kasar Lebanon inda ta kai hare-hare har kan  rijiyoyin ruwa na mutane kasashen Syriya da Lebanon da suke lardin. Hare-haren sun kai ga shahadar mutane 12 da kuma daruruwan da suka ji rauni.

Tashar talabijin ta Al-manar ta nakalto majiyar kungiyar na fadar haka, ya kuma kara da cewa wadan nan hare-re suna da hatsari, don da alamun gwamnatin kasar Amurka wacce ta dauki hakkin kula da tsagaiuta budewa juna wuta wanda aka cimma da HKI ta mika mata ragamar al-amura na tayi duk abinda taga dama.

A danyan bangaren kuma inji bayanin, jami’an gwamnatin kasar Lebanon basa magana kwata-kwata a kan wannan al-amarin. Amma kungiyar da kuma mutane kasar Lebanon ba abinda wannan yake kara masu sai karfin guiwa da kuma tabbata kan abinda suka yi Imani da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted