Ali Mohammad Sabeghi, tsohon jami’in bangaren al-adu na ofishin jakadancin kasar Iran a kasar China ya karbi kyautar ‘Jakadan Abota’ na kasar China a wannan shekara ta 2025M. A bikin bada irin wannan kyauta karo na biyu.
Labarin ya kara da cewa dangantaka tsakanin JMI ta kuma China yana daga cikin abota mafi kyau tsakanin kasashen yankin da kasar China. Labarin ya kara da cewa girmama kasar Iran ta wannan kyautar yana daga cikin al-amuran da zasu kara dankon zumunci tsakaninta da Tehran.
Hukumar al-adu na kasar China ta bayyana cewa ta samar da irin wannan kyautar ne don karfafa danganta kasar China da da sauran kasashen duniya musamman kasashen Asia.
A shekarar da ta gabata dai wannan kyauta ta shiga hannun kasar Pakisatan ne, wanda aka bawa Zafar Ud-deen Mahmood.