An Kashe Jami’in Sojan HKI A Gaza

Rundunar sojan mamaya ta sanar da kashe  daya daga cikin jami’an sojojinta dake karkashin rundunar “Golani” a yankin Khan-Yunus dake Gaza. Da safiyar yau Juma’a

Rundunar sojan mamaya ta sanar da kashe  daya daga cikin jami’an sojojinta dake karkashin rundunar “Golani” a yankin Khan-Yunus dake Gaza.

Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin mamayar HKI su ka snar da cewa wani daga cikin mayakansu mai mukamin  Captain ya halaka a Gaza, kuma tuni sun bude bincike akan abinda ya faru.

Rahoton tashar talabijin din ” Cane” ta HKI ya ambaci cewa, sojan da aka kashe yana cikin wadanda su ka kai hari a garin Khan-Yunus a jiya Alhamis.

Sojojin mamaya sun kai hari ne a cikin wani gida a ci gaba da kashe ‘yan gwgawarmaya da suke yi, sai dai ginin gidan ya rufta da su, bayan da nakiyar da take cikinsa ta fashe.

Tun a jiya Alhamis ne dai kafafen watsa labarun na HKI su ka fara Magana akan cewa sojojin da suke Gaza, suna fuskantar yanaki mai tsanani, da hakan yake nufin cewa an halaka wani adadi nasu.

An ga jirgin sama mai saukar angulu yana shawagi a yankin da aka yi kazamin fada a tsakanin ‘yan gwgawarmaya da kuma sojojin mamaya.

A cikin kwanakin bayan nan dai ‘yan gwgawarmaya suna kara samun nasarar halaka sojojin HKI da suke yi wa al’ummar yankin kisan kiyashi da kuma jikkata wani adadi mai yawa nasu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted