Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattaunawa da Firay minister da kuma yerma mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya Mohammad bin Salman kan karfafa dankon zumuncim tsakanin kasashen biyu da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran Aragchi ya hadu da dan sarkin ne a Makka, a ranar talata , kafin haka ministocin harkokin wajen kasashen biyu wato Faisal Bin Farhan kan wadan nan batutuwan. Dangantaka tsakanin kasashen biyu masu karfi a yankin, ya shiga cikin tsarin JMI na makobta da farko.
Bin salman dangane rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da HKI da kuma Amurka, y ace yana fatan karshensa ya zama mai samar da zaman lafiya a mai dorewa a yankin.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran ya fadawa Bin salman kan cewa kasar Iran ta gode da yadda gwamnatin saudiya ta yi allawadai da hare-haren da HKI ta kaiwa Iran a yakin 12 da suka fafata.