Sojojin Yemen Sun Nutsar Da Jirgin Ruwan “Eternity” Dake Hanyar Zuwa HKI

Sojojin Yemen sun sanar da nitsar da jirgin ruwa “Eternity’ wanda yake hanyar zuwa tashar jiragen ruwan HKI ta Eliat, bayan da matukinsa ya ki

Sojojin Yemen sun sanar da nitsar da jirgin ruwa “Eternity’ wanda yake hanyar zuwa tashar jiragen ruwan HKI ta Eliat, bayan da matukinsa ya ki jin girgadin da aka yi masa.

Janar Yahya Sari ne ya bayyana cewa; Jirgin ruwan ya ki jin gargadin da aka yi masa na hana kowane jirgi wucewa zuwa tasoshin jiragen ruwan HKI.

Sanarwar sojojin kasar ta Yemen ta kunshi cewa, sun yi amfani da karamin jirgin ruwa maras matuki da kuma wasu makamai masu linzami guda shida domin dakatar da jirgin ruwan.

Sai dai, tun da fari sojojin na Yemen sun tseratar da matukin jirgin da ma’aikatan da suke cikinsa, tare da ba su kulawa ta kiwon lafiya.

Janar Sari ya ce; Suna daukar wannan irin matakin ne domin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, tare da jaddada cewa za su ci gaba da daukar wannan irin matakin har zuwa lokacin da za a kawo karshen killace Gaza da kisan kiyashin da ake yi musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted