Hukumar abinci ta duniya ta fara aikewa da kayan abinci zuwa kudancin Sudan, ta hanyar amfani da jiragen sama domin jefa kayan agaji ga mazauna Kudancin Sudan da sauran yankunan da suke a killace tun cikin watan Maris.
Tun watanni 4 da su ka gabata ne dai hukumar abincin ta duniya ta fara aikewa da kayan agaji a kudancin Sudan din, bayan da fada mai tsanani ya hana a iya bi ta hanyoyin kasa.
A gefe daya, shugabar kungiyar ta Abinci reshen Afirka Mary Elen macgroti ta ce, fada da ake ci gaba da yi a yankin ya haddasa karacin abinci, tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa domin magance wannan matsala.
Da akwi mutane kusan miliyan daya a yankin tekun Nilu da suke fuskantar yunwa mai tsanani, wasu 34,000 daga cikinsu yanayinsu ya fi tsananta.
Tun da yaki ya barke a kasar Sudan a 2023, masu bukatuwa da taimako suke kara yawa, da hakan ya tilastawa miliyoyi yin hijira zuwa kasashen makwabta da kuma a cikin gida.
A kasar Habasha kadai da akwai ‘yan hijirar Sudan da sun kai 50,000, kamar yadda hukumar ta ambata.
A cikin jahohin Nilul-A’ala, da Arewacin Junqali kadai, hukumar Abincin ta Duniya tana son kai wa mutane 470,000 taimakon abinci daga nan zuwa watan Ogusta.
Sai dai hukumar ta yi korafin karancin abinci, ta yadda ya zuwa yanzu yake da bukatuwa da dalar Amurka miliyan 274 daga nan zuwa karshen wannan shekara. Yunwa tana yin barazana ga rayuwar mutane miliyan 7.7 a kudancin Sudan, amma a halin yanzu, hukumar za ta iya ciyar da mutane miliyan 2.5 ne kadai.