Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen

Kakakin ma’aikatar harkokin  wajen kasar Iran Isma’el Baka’e ya yi allawadai da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu yankuna a kasar Yemen

Kakakin ma’aikatar harkokin  wajen kasar Iran Isma’el Baka’e ya yi allawadai da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu yankuna a kasar Yemen a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya litinin ya kuma yi tir da hare-hare kan a Hudaydah, Ras-Isa, as-Salif da kuma tashar wutan lantarki na Ras al-Kathib.

Har’ila yau Baka’ee ya yi allawadai da kai hare-hare kan cibiyar tattalin arziki na kasar ta Yemen a Hudaida, wadanda suka hada da kayakin jama’a wadanda suka hada da gadoji da hanyoyiu da tashar Jiragen sama, da tashar jiragen ruwa da kuma rumbunan ajiyar abinci. Wandanda gaba dayansu yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Hare-harin ranar Lahadi  dai sune na farko bayan kimani wata guda, sannan sun zo ne bayan da yahudawan suke ce wai sun kakkabo dukkan makamai masu linzami wadanda sojojin kasar Yemen suke kaiwa kan HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted