JMI Ta Bukaci Kungiyar Majalisun Dokoki Ta Duniya Su Kori HKI Daga Cikinta

Shugaban tawagar Iran a kungiyar hada kan majalisun dokokin kasashen duniya ya bukaci kungiyar ta yi tir da HKI saboda hare-haren da ta kai mata

Shugaban tawagar Iran a kungiyar hada kan majalisun dokokin kasashen duniya ya bukaci kungiyar ta yi tir da HKI saboda hare-haren da ta kai mata wanda ya keta dokokin kasa da kasa, ya kuma bukaci a koreta daga kungiyar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Manoorchehr Mottaki yana fadar haka a wata wasikar da ya aikewa shugaban kungiyar majalisun dokokin ta duniya wato IPU, shugaban Tulia Ackson, ya ce abin  fata shi ne kungiyar zata yi tir da HKI kan sabawa doka ta 2(4) na MDD.

Har’ila yau Mottaki ya bayyana cewa yana fatan Ackson zai sa a jingine samuwar HKI a kungiyar.

Ya ce majalisar majalisun ta tattauna dangane da hare-haren Amurka da HKI kan kasar Iran su kumka yi All..wadai da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted