Iran Tana Tababa da Ayyukan Hukumar Makamashin Nukl’ila Ta MDD Wato IAEA A  Halin Yanzu

Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata

Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran.

Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran  yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da ministan tsaro na kasar Saudiya Yerima Khalid bin Salman, ya kuma kara da cewa HKI ba kasashe abin amincewa ba. Musawi ya ce sojojin JMI a shirye suka su dakile dukkan hare-haren da HKI zata kawo nan gaba.

A wani bangare kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasa da kasa ta kuma MDD IAEA yace Iran tana iya sake fara aikin tace makamashin Uranium a cikin watanni masu zuwa . Rafael Grossi ya bayyanawa tashar talabijin ta CBS a ranar Lahadi kan cewa , bayana hare-haren Amurka kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran ba zamu iya cewa kome yak are kuma. Saboda ba wanda ya isa y araba kasar Iran daga fasahar nukliyar da take da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted