Kasashen Iran Masar Da Kuma Oman Sun Gudanar Da Taro A Oslo

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun tattauna a tsakaninsu a birnin Oslo inda suka halattar taron tattaunawa ta 22th da ake gudanarwa a birnin na Oslo babban birnin kasar Norway.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bangarorin biyu sun yi maganar rikice-rikicen da ke faruwa a yankin da kuma hanyar warwaresu.

Taron oslo na shekara shekara dai a wannan karon ya maida hankali ne kan abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya da kuma hanyoyin da yakamata abi don rage halin da ake ciki a yankin. Musamman matsalar yaki da kima kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza da kuma yadda HKI ta sabawa dukkan dokokin kasa da kasa a yakin.

Jaridar The National ta kasar Amurka ta bada labarin cewa kasashen Iran da masar wadanda basa da dangantakar Diblomasiyya na kimani shekar 40 sun tattauna batun maida huldar jakadanci a tsakaninsu, inda daga cikin ministan harkokin wajen Masar ya bukaci a shafin hoton Khalid Islam buli wanda ya kashe tsohon shugabann kasar Masar a shekara 1980 wanda aka sanya a kan wani babban titi a birnin Tehran. Har yanzun dai ba’aji ta bakin gwamnatinn kasar Iran kan hakan ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted