Falasdinawa Masu Yawa Sun Yi Shahada A Cibiyoyin Raba Kayan Agaji

Sojojin HKI sun kai hari akan Falasdinawan da su ka yi cincirindo domin karbar abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu.

Sojojin HKI sun kai hari akan Falasdinawan da su ka yi cincirindo domin karbar abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu.

Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin HKI su ka rika kai hare-hare akan cibiyoyin cibiyoyin raba agaji wadanda dama suna a karkashin kulawar su kansu ‘yan sahayoniyar da kuma Amurka. Har ila yau hare-haren sun shafi gidajen fararen hula a cikin wasu unguwanni na zirin Gaza.

Majiyar Asibitin “Audah” ta sanar da cewa an kai shahida 4 da kuma wadanda su ka jikkata sanadiyyar hare-haren na sojojin mamaya a wurin raba kayan agaji dake kan titin “Salahuddin” a tsakiyar zirin Gaza.

A arewacin yankin Gaza kuwa wasu samarin Falasdinawa 4 sun yi shahada bayan da jiragen yakin HKI su ka kai hari a kusa da makarantar “Usamatu Bin Zayd” dake yankin Safdhawi.

Wasu jiragen yakin na ‘yan mamaya sun kai wasu hare-haren a unguwar “Basrah’ dake birnin Gaza. Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko yin shahada.

A kusa da mashigar ‘al-Buraij’ ma sojojin mamayar sun kai hari da jirgin sama maras matuki akan mutane da suka yi cirko-cirko suna tsumayen kayan agaji.

Wasu wuraren da aka sami shahidai sun hada da sansanin ‘yan hijira na “Nusairat’ da “Muwasi” a Khan-Yunus, sai kuma  “Badhnus-samin”.

Tun a makwannin da su ka gabata ne dai MDD ta sanar da cewa ba za ta shiga cikin tsarin dake karkashin HKI da Amurka ba, na raba kayan agaji, saboda manufarsa korar Falasdinawa daga gidajensu. Ita kuwa kungiyar Hamas ta ce, wuraren na rabon agaji sun zama tarko kisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted