Afirka Tana Shirin Samar Da Maganin Kwalara Da Kanta

Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar. An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi

Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar.

An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa akan hanyoyin magance cutuka mabanbanta da su ka hada da riga-kafi.

Wadanda su ka halarci tattaunawar ta bidiyo sun hada shugabannin kasashen Angola, Namibia, Malawi da kuma DRC.

Shugaban kasar  Zambia Hakayinde Hichilema  ya bayyana cewa; Da akwai bukatar nahiyar Afirka ta fara samar da magunguna cikin gaggawa tare da dogaro da nahiyar wajen samar da kudaden da ake bukata domin yin hakan, saboda kaucewa dogaro da waje.”

Haka nan kuma shugaban kasar ta Zambia ya ce: Saboda kwalara idan ta barke ba ta san iyakar kasashe ba, ya kamata mu yi aiki tare da kuma samar da tsarin yin gargadi na gaggawa a tsakanin kasashen makwabta.”

Shi kuwa shugaban kasar Angola João Lourenço, wanda kuma shi ne yake rike da kambun jagorancin kungiyar nahiyar Afirka, ya bayyana cewa: ” Cutar kwalara ta fi karfin a dauke ta a matsayin wani yanayi na gaggawa da yake bijirowa a fagen kiwon lafiya, tana a matsayin kaulabale ne  mai girma dake hana ci gaba na tattalin arziki da bunkasar al’umma a nahiyar ta Afirka.”

Shi kuwa shugaban hukumar lafiya ta duniya : Adhanom Gibisos cewa ya yi; A cikin wannan shekarar ta 2025 a cikin nahiyar Afirka ne za yi kaso 1/3 na dukkanin kwalarar da za ta barke a duniya, kuma a cikin nahiyar ne dai za a sami mutuwar kaso 99% na jumillar wadanda cutar za ta kaseh a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted