Trump ya haramtawa ‘yan kasashen duniya 12 shiga Amurka

Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramtawa kasashen duniya 12 shiga Amurka a wani mataki da ya ce na kare kasar ne daga “yan ta’adda

Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramtawa kasashen duniya 12 shiga Amurka a wani mataki da ya ce na kare kasar ne daga “yan ta’adda na kasashen waje.

Wata takarda da fadar White House ta fitar a ranar Laraba ta ce haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yuni, ya shafi kasashen Afghanistan, Burma, Chadi, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, da kuma Yemen.

Baya ga hakan akwai wasu kasashe bakwai su ma da aka gindawa wasu sharudda da suka hada da Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da kuma Venezuela.

A cewar Amurka matakin bai shafi mutanen da balaguron su zuwa kasar ke da amfani ga muradun kasar ba.”

Haka ma  ‘Yan wasan kwallon kafa da za su fafata a gasar cin kofin duniya ta 2026, da za a gudanar a Amurka, Mexico da Canada, da kuma ‘yan wasa a gasar Olympics ta Los Angeles ta 2028, takunkumin ba zai shafe su ba.

Matakin dai na da nasaba ne da harin da aka kai a Colorado, in ji Donald Trump.

A ranar Lahadi, data gabata ce, wani mutum ya jefa abubuwa masu tayar da wuta a kan mahalarta tattakin mako-mako a jihar Colorado na nuna goyon baya ga ‘yan Isra’ila da ake garkuwa da su a zirin Gaza.

A cewar fadar White House, wanda ake zargi da kai harin ya shiga a Amurka ne “ba bisa ka’ida ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted