Sabon Firay Ministan Sudan Ya Bukaci Kasashen Dake Taimaka Wa “RSF” Da Su Daina

Sabon fira ministan kasar Sudan Kamil Idris ya yi kira ga kasashen waje masu taimaka wa dakarun daukin gaggawa “RSF” da su kawo karshen taimakon

Sabon fira ministan kasar Sudan Kamil Idris ya yi kira ga kasashen waje masu taimaka wa dakarun daukin gaggawa “RSF” da su kawo karshen taimakon da suke bawa masu aikata laifi.”

Idris wanda yake jawabin bayan kama aiki a jiya ya ce; Jami’an tsaro da kuma mahukuntan kasar ta Sudan suna da cikakken goyon baya a kasar don kawo karsehn ‘yan tawaye, masu dauke da makamai.”

Idris ya kuma ce; A shirye yake ya yi wa kasa aiki a cikin kekyawar anniyya da kwazo.”

Gwamantin kasar Sudan dai tana zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da taimaka wa dakarun kai daukin gaggawa “RFS” wacce ta dauki shekaru biyu tana fafatawa da sojojin kasar.

Wasu daga cikin  kasashen da Sudan take  zargi da hannu a tawayen na “RSF” sun hada da Chadi, Libya da Sudan Ta Kudu.

Wasu rahotannin suna nuni da cewa, suna bawa wannan kungiyar makamai ne ta kan iyakokin da su ka hada wadannan kasashe da Sudan.

Tun barkewar yakin basasa a kasar Sudan a ranar 15 ga watan April 2023, zuwa yanzu adadin mutanen da su ka rasa rayukansu sun kai 24,000, yayin da wasu fiye da miliyan 14 su ka zama ‘yan gudun gijira, miliyan 4 daga cikinsu sun fice daga kasar, zuwa kasashen makwabta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted