Kasashen AES zasu kafa kotun hukunta manyan laifuka ta kungiyar

Ministocin shari’a na Burkina Faso, Mali da Nijar sun amince da kafa kotun hukunta laif  uka da kare hakkin bil’adama ta kungiyar tarayyar kasashen Sahel.

Ministocin shari’a na Burkina Faso, Mali da Nijar sun amince da kafa kotun hukunta laif  uka da kare hakkin bil’adama ta kungiyar tarayyar kasashen Sahel.

Haka kuma za a gina wani gidan yari mai cikakken tsaro a yankin, mai alaka da wannan kotun, domin karfafa hanyoyin yaki da ta’addanci da aikata laifuka a yankin.

Sun bayyana hakan ne bayan taron da suka gudanar a birnin Bamako a ranakun 29 da 30 ga watan Mayu.

Kotun hukunta manyan laifuka da kare hakkin bil’adama a yankin Sahel A cewar shafin labarai na APANews, za ta dauki nauyin “duba laifukan cin zarafin bil’adama, laifuffukan yaki, kisan kiyashi da ta’addanci, halatta kudaden haram da kuma cin zarafi mai tsanani na ‘yancin dan adam da sauran manyan laifuka masu alaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted