Limamin Sallar Juma’ar Tehran Ya Jaddada Cewa: Babu Wanda Zai Dakatar Da Iran Tace Sinadarin  Uranium

Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya

Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Iran ba ta neman mallakar makamin nukiliya, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana ba. Ya kara da cewa: Iran tana inganta sinadarin Uranium kuma za ta ci gaba da yin hakan domin bunkasa harkokin ci gaban kasarta musamman harkar lafiya, wutan lantarki, likitanci, noma da sauransu.

Limamin Juma’ar Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Hakika dogaro da yarda da kai, a halin yanzu ta kai Iran ga duk harkokin bunkasa ci gaban kasarta, yana mai jaddada cewa: Za a ci gaba da sarrafa sinadarin Uranium a kasar Iran duk kuwa da matsayar adawa da kasashen yamma suke nunawa kan haka.

A cikin hudubar sallar Juma’ar a jiya Juma’a Ayatullah Khatami ya kara da cewa: “Al’umma sun ga yadda suke son mayar da Iran baya a fagen makamashin nukiliya, suna cewa bai kamata Iran ta kasance ta mallaki na’urar taken Uranium koda guda daya ba, amma godiya ga Allah da kokarin masana kimiyya na kasar Iran, kasar ta samu gagarumin ci gaba a wannan fanni na kimiyya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted