Mamakon ruwan sama da ya sauka a jihar Rivers ta Najeriya ya yi gyara, tare da daukar rayukan mutane 25,kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasar ta sanar.
Ruwan da ya sauka a garin Okrika ya haddasa zaizayar kasa,wacce ta binne gidaje da dama, da kuma yin awon gaba da mutane.
Masu ayyukan ceto sun ce har yanzu ana ci gaba da gano gawawwakin mutane a karkashin baraguzai. Haka nan kuma mutane da dama sun rasa matsugunansu.
Duk da cewa ana ci gaba da ayyukan ceto said ai har yanzu da akwai yankuna da ba za a iya shiga cikinsu ba saboda sun yi lungu.