Iran Ta Yi Watsi Da Jita-Jitar Cewa Za Ta Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya sanar a marecen jiya Laraba cewa, Iran za ta iya dakatar da tace sanadarin Uranium a

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya sanar a marecen jiya Laraba cewa, Iran za ta iya dakatar da tace sanadarin Uranium a karkashin yarjejniyar da za a iya kullawa da Amurka.

Kakakin ma’ikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Baka’i ya yi watsi da labarin da kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya watsa na yiyuwar dakatar da tace sanadarin “Uranium’ yana mai kara da cewa; zai ci gaba babu kakkautawa, kuma ba abinda za ma za a yi tayi ba.”

Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato Baka’i yana cewa; labarin na Reuters, ba komai ba ne sai farfaganda ake maimaitawa, da kuma an sha kore gaskiyarta.

Kamfanin dillancin labarun na “Reuters’ kamar yadda ya saba, ya ambato wata majiya Iran, wacce bai ambata kowacece ba, tana cewa za a dakatar da tace sanadarin Uranium din na wucin gadi, saboda a sakar mata kudadenta da ake rike da su.

A lukuta da dama dai jami’an kasar Iran sun sha ambata cewa batun tace sanadarin “Urani’um” wani abu ne da za a ci gaba da yinsa a cikin Iran,an cimma yarjejeniya, ko a’a.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa; Iran ba ta dauki batun tace Urani’um abin wasa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted