Amurka za ta hana ‘’visa’’ ga daliban dake sukanta a shafukan sada zumunta

Gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta umarci ofisoshin jakadancinta da ke faɗin duniya su dakatar da bai wa dalibai da sauran mutane da ke neman

Gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta umarci ofisoshin jakadancinta da ke faɗin duniya su dakatar da bai wa dalibai da sauran mutane da ke neman bizar ziyara zuwa kasar.

Gwamnatin ta ba da umarnin ne yayin da take fadada shirin binciken bada bisa ta hanyar tantance abubuwan da mutum ke wallafawa a shafukan sada zumunta, musamma dalibai.

Wasu daliban kuma da tuni suke Amurka an kwace bizarsu saboda shiga gangamin nuna goyon-bayan Falasdinawa.

Wannan na daga cikin matakan da Trump ke dauka na hana manyan makarantun Amurka da suka yi fice wajen dogaro da kudaden makaranta da suke samu daga daliban ketare.

Kafin wannan lokaci fadar gwamnatin Amurka White House ta ce gwamnatin Trump ta bukaci dukkanin ma’aikatun Amurka su datse tallafin da suke bai wa jami’ar Havard da suke amfani da shi wajen bada tallafin karatu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted