An Gargadi Shugaban Amurka Dangane Da Fadawa Iran Da Yaki

Jaridar ;The HIL’ ta kasar Amurka wacce take bada labaran majalisa da siyasar gwamnatin Amurka ta gargadi gwamnatin shugaba Donal Trump kada ta sake irin

Jaridar ;The HIL’ ta kasar Amurka wacce take bada labaran majalisa da siyasar gwamnatin Amurka ta gargadi gwamnatin shugaba Donal Trump kada ta sake irin kuskuren da shugaban kasar Iran Sadam Hussain yaki na fadawa kasar Iran da yaki, tare da tsammanin cewa a cikin yan kwanaki zai ga faduwar jaririyar gwamnatin kasar Iran a lokacin. Amma sai wankin hula ya kai masa dare, inda ya share shekaru 8 yana fafatawa da mutanen kasar Iran ba kuma tare da samun nasarar ba.

Jaridar ta kara da cewa Iran ba kasace wacce tana dab da faduwa ne sai aje a karasa faduwarta ba. Kasashen wacce kan mutanen kasar a hade yake a duk lokacinda na waje yayi kokarin mamayar kasar.

Labarin ya kara da cewa, jaridar ta bukaci gwamnatin Trump kada ta sake kuskuren da sadan Hussain yayi kuma ta kasar ta laluma ta hanyar diblomasiyya, don warware dukkan matsalolin da ke tsakaninsu da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted