Rasha Ta Tarwatsa Makaman Ukiraniya A Tashar Jiragen Ruwa Ta Odessa

Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100

Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100 dake dauke da makamai a tashar jiragen ruwa ta Odessa.

Sanarwar ta kuma kunshi cewa makaman da sojojin na Rasha su ka tarwatsa sun hada kananan jiragen ruwa na yaki na kai farmaki da ba su da matuki, jiragen sama marasa matuki, da kuma albarusai. Haka nan kuma harin ya shafi manyan dakunan ajiye makamai a cikin tashar jiragen ruwan na Odessa.

Sanadiyyar wannan harin harshen wuta ya tashi wanda ya dauki lokaci yana ci.

 A gefe daya an yi musayar fursunoni a tsakanin sojojin Rasha da kuma na Ukiraniya wanda shi ne mafi girma tun da yaki ya barke a tsakanin kasashen biyu.

A wani gefen, har yanzu ana ci gaba da Magana akan tsagaita wutar yaki, da Amurka take son ganin ya faru, saboda kare manufofinta na dibar albarkun kasar ta Ukiraniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted