Wasu Yahudawa Sun Hana Kayakin Agaji Shiga Yankin Gaza

Bayan watannin kimani biyu da rabi wanda gwamnatin HKI suka hana kayakin abinci da magunguna shiga yankin zirin Gaza, a jiya talata, gwamnatin Natanyahu ta

Bayan watannin kimani biyu da rabi wanda gwamnatin HKI suka hana kayakin abinci da magunguna shiga yankin zirin Gaza, a jiya talata, gwamnatin Natanyahu ta bada damar a shigo da wasu kadan da kayakin agajin, saboda takurawar wasu shuwagabnni a kasashen yamma.

Amma duk da haka a yau wasu yahudawa fararen hula sun hana wucewar wata mota makare da abinci shigowa zirin gaza daga kofar shiga yankin ta Karen Abu Salem.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda jerin gwanon motoci dauke da kayakin agaji zuwa gaza amma wasu yahudawa dauke da tutocin HKI sun zo sun tsaya a gaban daya daga cikinsu suna fadar cewa basu yarda a shigar da kayakin agaji zuwa gaza ba har sai sun mutu gaba daya.

 Sannan a dayan bangaren kuma sojojin HKI rike da bindigogi sun zuba masu ido suna kallo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted