Sojojin Sudan Sun Sanar Da Kammala “Tsarkake” Birnin Kahartum Daga Dakarun  RSF

A yau Talata ne dai sojojin Sudan su ka sanar da cewa, baki dayan jihar Khartum ta zama ‘yantacciya daga dakarun kai daukin gaggawa na                

A yau Talata ne dai sojojin Sudan su ka sanar da cewa, baki dayan jihar Khartum ta zama ‘yantacciya daga dakarun kai daukin gaggawa na                 ( RSF), bayan da  su ka kwace iko da fadar shugaban kasa dake cikin birnin a watan Maris.

Kakakin rundunar sojan Sudan ya sanar da cewa; Sojojin kasar da dukkanin bangarorinsu, suna ci gaba da sauke nauyin da yake kansu na fada da rundunar kai daukin gaggawa da masu taimaka mata a cikin yanki da kuma a fagen kasa da kasa.

Kakakin rundunar sojan kasar ta Sudan ya kuma ce; Sojojin na kasar Sudan suna samun nasarori a kowace rana.

Wata majiyar soja ta sanar da tashar talabijin din aljazira cewa; dakarun RSF sun kai hare-hare akan cibiyar kiwon lafiya ta soja dake garin Um-Durman’ bayan da sojoji su ka kwace iko da yankuna masu yawa a garin da kuma makamai da albarusai a unuwar “Saliha”.

Yaki a tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar kai daukin gaggawa ya barke ne dai a tsakiyar watan Aprilu na 2023,wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan fiye da mutane 20,000 da kuma tilastawa wasu mutane miliyan 15 yin hijira, kamar yadda MDD ta bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted