Pezeshkian : Zaman lafiya muke nema, ba yaki ba

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya mayar da martani ga shugaba Donald Trump na Amurka, yana mai cewa Iran kasa ce son zaman lafiya ba

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian, ya mayar da martani ga shugaba Donald Trump na Amurka, yana mai cewa Iran kasa ce son zaman lafiya ba yaki ba.

Zaman lafiya muke nema, ba yaki ba; Su ne ke haifar da rikici.

Muna fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar nan da ma makwabtanmu, inji shugaba Pezeshkian.

Muna neman ‘yan uwantaka da daidaito tsakanin kasashen Azarbaijan, Rasha, Afghanistan, Pakistan, Iraki da Saudiyya, in ji shugaban na Iran a, yayin da yake ishara da kalaman Trump.

Trump yana ganin zai iya yi mana barazana, ya sanya mana takunkumi, da kuma yin magana game da hakkin dan Adam, amma a lokaci guda suna da hannu a tashe-tashen hankula da laifuffuka a yankin.

Pezeshkian ya kira Iran da kasashen yankin abokai, ‘yan’uwa da dangi, sannan ya kara da cewa:

Kurdistan, Azerbaijan, Turkmenistan, Balochistan – mu duka iyali daya ne.

 Amma suna son su sa mu gaba da juna don biyan bukatunsu.

Ba za mu yi fada a tsakaninmu ba, domin muna daukar mutanen yankin a matsayin ’yan uwanmu.

Saudiyya kasa ce ta Musulunci, tushen Musulunci – ta yaya za mu yi jayayya da ita? Amma yana son ya dora Larabawa a gefe daya mu kuma a daya bangaren. Yana kokarin haddasa fitina a yankin, amma ba za mu bari ya yi haka ba, inji shugaban kasar ta Iran a raddi ga shugaba Trump na Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted