Iran Da Japan Sun Kara Zurfafa Dankon Zumunci Da Ke Tsakaninsu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan na farko Hiroyuki Namazu a nan birnin Tehran a

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan na farko Hiroyuki Namazu a nan birnin Tehran a jiya Talata inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran da suka shafi kasashen biyu na harkokin kasuwanci da kuma wasu bangarori, sannan tare da tattauna irin sauye-sauyen da ake samu a yankin da kuma abinda ya zama lazimi ga kasashen biyu su yi a wannan halin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasashen biyu sun kara jaddada bukatar kasashen su karfafa dangantaka da ke tsakaninsu.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan ya fada a taron kwamitin hadin guiwa na kasashen biyu kan cewa kasar Japan ta zabi zurfafa dangantaka da kasar Iran duk tare da matsalin lambar da Washington takeyi na nisansar kasar ta Iran.

Hamazu ya kammala da cewa Japan tana son fadada dangantakar tattalin arziki da JMI wanda suka hada da kasuwancin a bangarori daban-daban. Haka ma a bangaren tsaro da ya shafi yankin Asia gaba daya. Wannan dai yana faruwa ne a dai-dai lokacinda Washington ta kara kababawa kasar Iran sabbin takunkuman tattalin arziki a ranar litinin da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted