Gaza: Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A  Yau Asabar

Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama.  Mutane 4 sun

Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama.

 Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza.

Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da asubahin yau Asabar akan wani gidan da yake a sansanin ‘yan hijira da “Mukhayyam-Shati’i.” da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai 3 da jikkata wasu da dama.

Majiyar Falasdinawa ta kuma ambaci cewa, da asubahin yau Asabar sojojin HKI sun tarwatsa wasu gidaje a yankunan da suke gabashin birnin Kudus.

 Dama a jiya Juma’a jiragen yakin HKI sun kai hari akan wata makaranta da take kunshe da ‘yan hijira na  Yarmuk dake tsakiyar birnin Gaza wanda shi ma ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3.

A tsakiyar yankin na Gaza kuwa, manyan bindigogin HKI sun kai hare-hare a gabashin sansanin ‘al-Nusairat”.

A jiya kadai, Falasdinawa 48 ne su ka yi shahada a wasu hare-hare biyu da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa gidaje biyu a yankunan “Murtaji” da “al-fakhari” dake cikin garin “Khan-Yunusu” a kudancin zirin Gaza.

A efe daya, sojojin HKI suna ci gaba da tilastawa Falasdinawan yin hijira daga yankunan “Turkiman, da Jadid da suke a Arewacin unguwar Zaytun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted