HKI Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare A Unguwar Dahiya Junubiyya Na Birnin Beirut Na Kasar Lebanon
Jiragen yakin HKI sun jaddada kai hare hare a unguwar Dahiya Junubiyya na birnin Beirut a jiya Jumma’a da wasu yankuna a kudancin kasar ta Lebanon.
Tashar talabijin ta Al-Alam a nan birnin Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare har sau 4 yankin Bir-Abd, Alghubair, da haratul Harik duk a unguwar Dahiya Junibiyya na birnin Beirut. Banda haka sun kai wasu hare haren a kan wasu yankuna a cikin birnin.
Labarin ya kara da cewa gobara ta tashi a wasu ginegine a wadannan unguwanni, sannan mutane da dama sun kai ga shahada, wasu kuma suka ji rauni.
Mutane 11 ne suka kai ga shahada a hare-haren a unguwar Najah, sannan mutane 18 ne suka yi shahada, mafi yawansu mata da yara a garin Falawi na kudancin kasar ta Lebanon.
Har’ila yau Jiragen yahudawan sun kai hare hare a kauyukan Baraliya, da Durus da kuma Yahmar.