A jiya Juma’a ne sojojin kasar ta Yemen su ka sanar da kai wa HKI hari da makami mai linzami mai cin dogon zango wanda ya sauka akan sansanin sojan ‘yan sahayoniya na sama na “Navatim” a yankin Nakab a kudancin Falasdinu.
Kakakin sojan Yemen Janar Yahya Sari ne ya sanar da kai harin da makami mai linzami wanda ya fi sauti sauri da su ka bai wa suna: “Falasdinu 2”.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa makamin ya sauka daidai inda aka tura shi.
Har ila yau Janar Yahya Sarii ya ce; Ba za mu daina kai hare-haren da muke kai wa ba har sai idan ‘yan sahayoniya sun kawo karshe hare-harensu a Gaza da kuma Lebanon.”
Sojojin Yemen sun shiga cikin masu taya Falasdinawa fada tun farkon da HKI ta shelanta yaki akan Gaza, inda suke kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.
Bugu da kari, sojojin Yemen sun hana wucewar jiragen ruwa da suke zuwa HKI ta mashigar tekun “Red-Sea”.
A gefe daya dubun dubatar mutanen kasar ta Yemen sun yi gangami a birnin San’aa domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Gaza da Lebanon da suke fuskantar yaki mai tsanani daga HKI.