Rahotanni da suke fitowa daga birnin Beirut sun ambaci cewa jiragen yakin HKI sun kai hari da makamai masu karfin fashewa akan wani gini dake tsakiyar birnin Beirut.
Tashar talabijin din ‘al-mayadin’ ta bayyana cewa; Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu tsananin karfi akan wani gini mai hawa takwas dake unguwar ‘Basdha” a birnin Beirut da hakan ya yi sanadiyyar rushewar ginin baki daya.
Rahoton tashar talabijin din ya kuma ce; ginin da aka kai wa harin yana cike da fararen hula, kuma sauran gine-ginen da suke kusa da shi duk sun illata.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta ce, bayanan farko suna nuni da cewa mutane 4 ne su ka yi shahada, kuma wasu 23 sun jikkata.
Har yanzu ana cigaba da zakulo mutanen da suke a karkashin baraguzan ginin da ya zube kasa baki daya.