Tawagar Amurka da ta isa birnin Beirut ta tattauna da mahukuntan kasar akan batun tsagaita wutar yaki.
Jagoran tawagar ta Amurka Amos Hochstein ya bayyana cewa, tattaunawar da ya yi da shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ta haifar da Da, mai ido.
Har ila yau Amos ya karbi martanin da Lebanon ta mayar akan shawarar da aka gabatar ta tsagaita wutar yaki a tsakanin Lebanon da HKI.
Da safiyar yau Talata ne dai tawagar ta Amurka a karkashin Amos Hochstein ta isa birnin Beirut domin jin ta bakin mahukuntan kasar akan shawarar da Amurka da HKI su ka gabatar na tsagaita wutar yaki.
Sai dai majiyoyin diplomasiyya sun bayyana cewa, sharuddan da suke cikin shawarwarin sun bai wa HKI damar kai hare-hare a Lebanon a duk lokacin da ta ga dama, lamarin da ko kadan Lebanon da gwagwarmayar Hizbullah ba za su laminta da shi ba.