Makarantan alkur’ani mai girma na kasar Iran da suke halartar gasar da ake yi a kasar Kuwaiti suna samun matsayi da kuma yabo daga al’ummar kasar ta Kuwaiti.
Jakadan Jamhuriyar Musulunci a kasar Kuwaiti ya rubuta a shafinsa na X cewa: Makarantan kur’ani Iraniyawa sun ja hankalin al’ummar kasar Kuwaiti ta hanyar kyautata karanta littafin Allah, suna yin tarayya a gasar da ake yi a Kuwaiti wacce ita ce karo na 13. Daga cikin mahalarta zaman gasar da akwai ministan harkokin addini Muhammad al-Wasmi da kuma jakadan Iran a Kuwaiti Muhammad Tutunchi.
Da akwai mahardatan kur’ani su 127 da suke halartar gasar daga kasashe 75,kuma suna yin tarayya matakai daban-daban na karatun littafin Allah mai tsarki.
Daga jamhuriyar musulunci ta Iran da akwai mahardata da su ka hada Muhamamd Ridha Zahiri, da Habib Sadakat,sai kuma Muhammad Husain Malaki Najad.
A gefe daya kuma an gudanar da baje koli na kur’ani mai girma wanda ya hada baje rubuce-rubuce na kur’ani masu tsawon tarihi ko kuma wadanda aka kyautata rubutunsu.