Kasar Rasha ta hau kan kujerar naki wato veto don nuna adawa da matakin da kasar Birtaniya ta dauka kan Sudan
Kasar Rasha ta yi amfani da ikonta na veto, a jiya Litinin, wajen yin watsi da wani daftarin kudiri a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya wanda ya bukaci a gaggauta dakatar da yaki a Sudan tare da kare fararen hula daga rikicin da ya tarwatsa kasar tun daga watan Afrilun shekara ta 2023.
Daftarin kudurin ya yi kira ga bangarorin da suke fada da juna da su gaggauta tsagaita bude wuta tare da sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta ba da damar ci gaba da rage wutar rikici da nufin amincewa cikin gaggawa kan tsagaita bude wuta a fadin kasar.
Kamar yadda kudurin ya yi kira ga bangarorin biyu da su aiwatar da alkawurran da suka dauka a shekara ta 2023 na kare fararen hula, dakatar da hana cin zarafin mata da ke da alaka da rikice-rikice, da ba da damar kai daukin kayan jin kai cikin gaggawa da aminci ba tare da samun wata cikas ba a ko’ina cikin Sudan.