Manyan jami’an soji na kasashen Iran da Azabaijan sun jaddada aniyar kasashensu na ci gaba da hadin gwiwar soji da tsaro a tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna.
Mataimakin babban hafsan hafsan sojin kasar Iran Birgediya Janar Mohammad-Reza Ashtiani da Manjo Janar Farid Aliyef ne suka bayyana hakan a yayin taron kwamitin hadin gwiwa na soja da tsaro karo na hudu a birnin Tehran na kasar Iran a wannan Litinin.
Ashtiani ya jaddada cewa, kasancewar alaka mai zurfi a tsakanin kasashen biyu ta taimaka wajen inganta matakin hadin gwiwa tsakanin kasashensu.
Ya kara da cewa, “Tsarin dangantaka da mu’amala tsakanin kasashen biyu ya zama wani dandali na samun nasara da kuma samun damar inganta hadin gwiwarsu cikin tsarin manufofin kasashen da muradunsu,” in ji shi.
Jami’in na Iran ya bayyana Jamhuriyar Azarbaijan a matsayin kasa mai matukar muhimmanci kuma mai tasiri” a cikin manufofin tsaro da harkokin waje na Jamhuriyar Musulunci.
Ya bayyana yanayin da ake ciki a yankin Kudancin Kaucasus a matsayin wani muhimmin yanayi a wajen Jamhuriyar Musulunci ta fuskar tsaro.
A nasa bangaren, Aliyef shi ma ya amince da wanzuwar manyan al’amura na hadin gwiwa da alaka tsakanin al’ummomi da kuma gwamnatocin kasashen biyu.
Ya bukaci da a kara yin hadin gwiwa a bangaren samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a daukacin yankin.
Ya ba da misali da gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa da kuma ayyukan hadin gwiwa na soji da ke gudana tsakanin kasashen a matsayin misali na hadin gwiwa.