Bangarorin gwagwarmayar Palasdinawa sun yi juyayin shahadar jami’in hulda da kafafen yada labarai na kungiyar Hizbullah, shahid Muhammad Afif, tare da yaba wa gudunmawar ad ya bayar a matsayin “muryar tsayin daka mai karfi, wadda ta dagula shirin makiya yahudawan sahyuniya.
A yammacin jiya bangarorin gwagwarmayar Palasdinawa sun yi juyayin shahadar jami’in hulda da manema labarai na kungiyar Hizbullah, Shahid Kwamanda Muhammad Afif.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta yi kakkausar suka kan wannan aika-aikar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata, tana mai jaddada cewa kisan gillar da aka yi wa wananna babban jami’I na Hizbullah ba zai dushe muryar gaskiya ta ‘yan gwagwarmaya ba.
Kungiyar ta yi nuni da cewa shahid Afif, tare da bayyaninsa a kafafen yada labarai masu karfafa gwiwa daga tsakiyar yankin kudancin birnin Beirut, kuma a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan kasar Labanon, wannan gagarumin matsayi da jarunta nasa na wakiltar “muryar ‘yan gwagwarmaya ne baki daya, kuma wannan matsayi nasa ya dagula lamarin ‘yan mamaya, tare da fallasa laifuffukansu, da kore labaran karya da suke yadawa, tare da bayyana labarai na gaskiyar abin da ke faruwa.
Ta kuma jaddada cewa yunkurin Isra’ila na yi masa kisan gilla, ya bayyana zurfin tasirinsa da kuma aikin da yake gudanarwa.
A nata bangaren, Harkar Jihad Islami daga babban sakataren kungiyar , ya mika sakon ta’aziyya ga babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem da kuma na kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon kan shahadar Muhammad Afif.