Shugaban Bangaren Watsa Labaru Na Hizbullah Ya Yi Shahada

Babban Sakatare Jam’iyyar Ba’as ta Lebanon Aliyul-Hizaji ya sanar da shahadar Haj Muhammadu Afif wanda shi ne shugaban bangaren watsa labaru na kungiyar Hizbullah. Ali

Babban Sakatare Jam’iyyar Ba’as ta Lebanon Aliyul-Hizaji ya sanar da shahadar Haj Muhammadu Afif wanda shi ne shugaban bangaren watsa labaru na kungiyar Hizbullah.

Ali Hijazi ya ce, Haji Afif ya yi shahada ne sanadiyyar harin da Isra’ila ta kai a yankin “Ra’asun-Nab’i” dake cikin Beirut a lokacin da yake ciki.

Rahotannin farko sun bayyana cewa, wasu mutanen 3 sun jikkata, sai dai daga baya an tabbatar da shahdar mutane 5 daga cikinsu har da Haj Muhammad Afif.

Ali Hijaz ya kuma ce abinda HKI take son yi a wanann lokacin shi ne rufe bakin gwgawarmaya, domin aikin Haji Afif shi ne watsa labaru ba yaki a filin daga ba.

Ali Hajizi ya kuma ce; Tabbas muna tare da gwgawarmaya, kuma tabbas za mu yi nasara, domin muna da yakini akan haka.

Shugaban jam’iyyar ta “Ba’as” ya ce, gidan da aka kai wa hari nasu ne, kuma babu mayaka a cikinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments