Hare-haren Hizbullah Sun Yi Barna Mai Yawa A Birninn Haifa

Hare-haren da Hibzullah ta kai   a yau Lahadi sun shafi sansanonin soja da kuma matsugunan ‘yan share wuri zauna da sojoji su ka mayar da

Hare-haren da Hibzullah ta kai   a yau Lahadi sun shafi sansanonin soja da kuma matsugunan ‘yan share wuri zauna da sojoji su ka mayar da su barikokin soja.

A bayanin farko da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa; A karkashin taimakawa Falasdinawa da kuma kare mutanen Gaza da goyon bayan gwgawarmayarsu    haka nan kuma mutanen Lebanon,dakarun gwagwarmayar musulunci sun kai hari akan sansanin rundunar Golani ta “Ma’aliyah”.

Sanarwar ta kuma ambaci kai wasu hare-haren da makamai masu linzami akan cincirindon sojojin mamaya a gafen garin Khayam, sai kuma sansanin Kiriyot dake kudancin garin Haifa.

Bugu da kari wasu jerin hare-haren na Hizbullah a cikin Falasdinu dake karkashin mamaya sun haddasa kadawar jiniyar  gargadi a cikin garuruwan  Akka, da Kiryot.

A wani labarin da kafafen watsa labarun HKI su ka watsa sun bayyana cewa; Wasu mutane uku sun jikkata sanadiyyar faduwar makamai masu linzami a yankin Jalil.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments