Gwamnatin mulkin soja a Nijar ta soke lasisim wata kungiyar agaji ta Faransa

Gwamnatin soja a Nijar ta haramtawa wata hukumar ba da agaji ta Faransa yin aiki a cikin kasar sakamakon takun-saka da Paris. Gwamnatin mulkin sojan

Gwamnatin soja a Nijar ta haramtawa wata hukumar ba da agaji ta Faransa yin aiki a cikin kasar sakamakon takun-saka da Paris.

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sanar da haramtawa hukumar hadin kai da ci gaban kasa ta Faransa wato ACTED yin aiki a cikin kasar sakamakon takun sakar da ke tsakaninsu da Paris, baya ga soke izinin aiki na wata kungiyar agaji mai suna Niger Welfare Initiative.

Ma’aikatar harkokin cikin gida a Nijar ta sanya hannu kan matakin janye lasisin gudanar da ayyukan hukumar ba tare da bayar da wani karin haske ba.

Hukumar tana aiki a Nijar tun 2010, in ji Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press, inda ta yi aiki musamman don taimaka wa wadanda suka rasa matsugunansu sakamakon hare-hare da makamai da kuma bala’o’i na yanayi.

Shugaban majalisar mulkin rikon kwarya a Nijar, Janar Abderrahmane Tiani, ya zargi Faransa da neman tada zaune tsaye a kasarsa, ta hanyar sanya wakilan leken asiri na Faransa daga wasu kasashe domin gudanar da ayyukan zagon kasa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments