Dakarun Amurka sun kai munanan hare-hare a kan sojojin Siriya a rana ta biyu a jere.
Tashar talabijin ta al-Mayadeen ta kasar Labanon ta bayyana cewa, harin da Amurka ta kai da sanyin safiyar Larabar nan ya afkawa wasu wurare a wajen birnin al-Bukamal da ke lardin Dayr al-Zawr da ke gabashin kasar Siriya kusa da kan iyakar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kai hare-hare ta sama a wuraren da dakarun hadin gwiwa na Syria a yankin al-Jam’iyat da ke birnin al-Bukamal, inda ta kara da cewa mutane uku ne suka mutu tare da jikkata wasu biyar.
Babban kwamandan Amurka (CENTCOM) ya bayyana a cikin wata sanarwa a shafinta na sada zumunta na X cewa an kai harin ne a “wurin ajiyar makamai na kungiyoyin da suek dangantawa da ‘yan tada kayar baya.”
Sanarwar ta ce an kai harin ne a matsayin martani ga harin makami mai linzami da aka kai kan jami’an Amurka a Patrol Base Shaddadi a arewa maso gabashin Syria, wanda ta ce bai yi lahani ga wurin ba, ko kuma jikkata ga sojojin Amurka ko na kawancen.