A wata sanarwa da dakarun “Kassam” su ka fitar a jiya Talata sun sanar da cewa sun kai hare-hare har sau 10 akan sojojin HKI da su ka yi sanadiyyar kashe da kuma jikkata da dama daga cikinsu.
A gefe daya sojojin HKI suna cigaba da yin kisan kisan kiyashi a Gaza, inda a jiya kadai adadin wadanda su ka yi shahada ya kai 64.
A kudancin Gaza, jiragen HKI sun kai hare-hare sau uku a kudancin birnin Gaza da safiyar yau Laraba. A rukunin gidajen “Nusairat” kuwa jiragen na HKI sun kai wani harin sa’oi kadan da su ka gabata, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 2 da kuma wani adadi mai yawa na mutane da su ka jikkata.
A jabaliya ma jiragen yakin na HKI sun kai hari akan wani gida, da ya jikkata mutane da dama.
A can Rafah, kuwa sojojin HKI sun kai hari da jirgi maras matuki wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 11.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; jumillar adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 64 a cikin sa’oin da su ka gabata.
Daga fara yakin Gaza zuwa yanzu adadin Falasdinawa su ka yi shahada sun kai 43,000 da 665. Wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 103 da 76.