Iran ta soki gazawar matakan kasa da kasa wajen dakatar da hare haren Isra’ila a Gaza da kuma Lebanon.
Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref ne ya bayyana hakan a jawabinsa gun taron hadin gwiwa karo na biyu na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.
Mista Aref ya bukaci da a dauki matakin gama gari na Shugabannin Musulunci da na Larabawa domin cimma wannan manufa.
Mohammad Reza Aref ya bayyana jin dadinsa ga kasar Saudiyya da ta shirya wannan muhimmin taro, a wani yanayi da ke da nasaba da halin da ake ciki a yankin.
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya jaddada hakkin cin gashin kan al’ummar Falastinu da ake zalunta.
Mr. Aref ya ce jajircewa ko gazawar Majalisar Dinkin Duniya da sauran cibiyoyin kare hakkin bil’adama na rashin daukar kwararan matakai na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawan ya nuna halin ko in kula da kasashen duniya suka kan kisan gillar da aka yi wa mutane sama da 50,000 da ba su ji ba ba su gani ba, kuma a halin yanzu ana ci gaba da aikata irin wannan ta’asa a Lebanon tare da goyan baya da tallafin Amurka.
Don haka, Aref ya bayyana bukaci shugabannin musulmi da na larabawa da su himmatu wajen ganin an “Kawo karshen ta’addancin da Isra’ila ke ci gaba da yi, a Falastinu da Lebanon,”