Koriya ta Arewa ta amince da yarjejeniyar tsaro mai cike da tarihi da kasar Rasha.
Yarjejeniyar “An amince da ita ne ta hanyar wata doka” da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya sanya wa hannu jiya Litini, inji kamfanin ndilancin labaren Koriya ta arewar KCNA.
Matakin dai na zuwa ne kwana guda bayan sanarwar da Moscow ta fitar cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kare juna da Pyongyang.
A ziyarar da Putin ya kai Pyongyang a watan Yuni, yarjejeniya ta tsakanin wadannan kasashen biyu, ta tanadi daukar matakin “taimakon soji cikin gaggawa” a yayin harin da aka kai wa daya daga cikin kasashen biyu.
Yarjejeniyar ta kuma sa kasashen biyu su hada kai a duniya wajen adawa da takunkuman kasashen yamma.