Kungiyar Hamas ta aike da sako zuwa ga zaman taron kasashen musulmi da na Larabawa tana kira gare su ga muhimman bukatunta
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira ga sarakuna da shugabanni da jagororin al’umma da suka hallara a wajen taron hadin gwiwa na kasashen Larabawa da Musulunci da ake gudanarwa a birnin Riyadh fadar mulkin kasar Saudiyya, da su kulla kawancen kasashen Larabawa da Musulunci na kasa da kasa domin matsa lamba kan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila kan wajabcin dakatar da yakin kisan kare dangi a Zirin Gaza da Lebanon.
Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Kungiyar Hamas a cikin sakon wasikarta ga zaman taron ta jaddada bukatar ganin wannan hadin gwiwa ta yi aiki wajen ganin an dakile hare-haren Gaza, da janyewa daga yankunan da aka mamaye, da baiwa al’ummar Falasdinu damar samun ‘yancin kai, tare da kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yancin gashin kanta tare da kasancewar Qudus a matsayin babban birninta gami da komawar ‘yan gudun hijirar Falasdinu garuruwa da kauyukan da suka yi hijira daga gare su.
Har ila yau kungiyar Hamas ta sake jaddada matsayinta na yin aiki mai kyau da duk wani shawarwari da ra’ayoyin da suke tabbatar da dakatar da wuce gona da iri, da janyewar ‘yan mamaya daga Gaza, da dawo da ‘yan gudun hijira zuwa matsugunansu da taimakawa al’ummarta da tilasta kawo karshen killace yankin da daukan matakin sake gina Gaza da kuma ganin an gudanar da musayar fursunoni bisa tubali na adalci da hakan zai tabbatar da dawo da yarjejeniyar da aka cimma a ranar 2 ga watan yulin da ya gabata, da kuma aiwatar da yarjejeniyar kudurin kwamitin sulhun Majalisar Dinikin Duniya mai lamba 2735.