Iran ta ce lokacin ya yi na a kori Isra’ila daga Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke yakin kisan kare dangi a Gaza da kuma cin zarafi da take yi wa kasar Labanon.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Taron dai na da nufin tattaunawa kan yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza kuma an yi shi ne gabanin wani taron gaggawa da aka shirya yi a yau litinin.
Ya ce lokaci ya yi da za a kori Isra’ila daga Majalisar Dinkin Duniya, saboda yadda gwamnatin kasar ke nuna adawa da halaccin Majalisar Dinkin Duniya, da suka hada da yage Yarjejeniyar ta, da kin maraba da Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da kuma haramta ayyukan hukumar UNRWA a yankunan data mamaye.
Ya kuma yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su kakabawa Isra’ila cikakken takunkumin makamai, tattalin arziki da kasuwanci da duk wasu cibiyoyi da ke goyon bayan mamayar gwamnatin Falasdinu.
Gharibabadi ya jaddada bukatar sake farfado da kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yaki da wariyar launin fata a kokarin gudanar da bincike kan laifukan gwamnatin Isra’ila.