Kungiyar Hizbullah ta ce sojojin Isra’ila sun kasa mamaye ko da kauye daya a kasar Lebanon tun bayan kaddamar da hare-haren wuce gona da iri a watan Satumba.
Tashar talabijin ta Aljazzera ta rawaito kakakin Hezbollah Mohammad Afif yana cewa “Bayan kwanaki 45 ana gwabza kazamin fada, har yanzu makiya sun kasa mamaye ko wani kauye guda na Lebanon.”
“Muna gaya wa makiya cewa ba za ku ci nasara a yakinku ba.”
Afif ya kara da cewa ikirari da Isra’ila ta yi game da gagarumin koma baya na tarin makamai masu linzami na Hezbollah “karya ce kawai”.
“Rundunar sojojinmu a fagen daga suna da isassun kayan aiki na dogon yaki,” in ji shi.
Kakakin ya kuma ce alakar kungiyar da sojojin kasar Lebanon “za ta kasance mai karfi” kuma zanga-zangar adawa da Isra’ila a duniya na nuni da cewa “Isra’ila ta koma saniyar ware”.