Sojojin HKI Sun Cigaba Da  Yin Kisan Kiyashi  A Kasar Lebanon

A daidai lokacin da yaki gadan-gadan da HKi ta shelanta akan Lebanon yake cika kwanaki 49, sojojin mamayar suna cigaba da yin kisan kiyashi. A

A daidai lokacin da yaki gadan-gadan da HKi ta shelanta akan Lebanon yake cika kwanaki 49, sojojin mamayar suna cigaba da yin kisan kiyashi.

A jiya Lahadi sojojin HKI sun kai munanan hare-hare a unguwar “Dhahiya” dake birnin Beirut da kuwa garuruwa mabanbanta da suke a kudancin Lebanon.

A yankin Jubail sojojin mamayar sun kai hare-hare da jirgin yaki wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 24 daga cikinsu da akwai kananan yara 7.

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Lebanon ta sanar da cewa, mutane 24 sun yi shahada daga cikinsu da akwai yara 7 sai kuma wasu 6 da su ka jikkata.

Wani dan majalisar kasar ta Lebanon Ra’id Baru’ayin wanda ya ziyarci wurin da aka kai hari, ya bayyana cewa ko kadan babu ‘yan gwagwarmaya a wurin. Ya kuma kara da cewa manufar ‘yan mamaya ita ce cusa tsoro a zukantan mutane.

A kudancin Lebanon din, sojojin mamaya sun kai wani harin ta jirgin sama a grin Adlun da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3. A garin Marja’iyyun kuwa ‘yan sahayoniyar sun kai hari da jirgin sama da shi ma ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama.

A wasu yankunan da jiragen saman ‘yan sahayoniya suke kai wa hari, ana samun wahala domin tantance adadin shahidai saboda mafi yawancinsu suna karkashin baraguzai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments