Jagora a kungiyar Hamas, Usama Hamdan, ya bukaci kasashen larabawa da na musulmi da su yi aiki tukuru domin ganin an kawo karshen yakin da HKI ta shelanta akan al’ummar Falasdinu.
Usama Hamadan ya kuma bayyana cewa, amfani da yunwa a matsayin makamin yaki yana cikin shirin da HKI take amfani da shi akan mutanen arewacin Gaza.
A jiya Lahadi da marece ne dai jagoran a kungiyar Hamas ya gudanar da jawabi daga birnin Beirut inda ya kara da cewa; A kowane lokaci ‘yan mamaya ne suke kawo cikas a shirin tsagaita wutar yaki, sannan kuma ya zargi Amurka da wasu kasashen turai da cewa sune abokan tarayyar HKI wajen aikata laifukan yaki na yi wa Falasdinawa kisan kiyashi.
Jagoran a kungiyar ta Hamas ya yi jinjina ga masu taya Falasdinawa yaki da su ka hada Lebanon,Yemen, da Iraki.
Dangane da abinda yake faruwa a kasar Holland, Usama Hamadan ya ce, matukar ba akawo karshen kisan kare dangin da ake yi a Gaza ba, to za a ga kwatankwacin abinda ya faru a Amsterdam a wani wuri a duniya.