Akalla mutum 27 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a gabashi da kudancin kasar Lebanon, in ji ma’aikatar lafiya.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, wani harin da Isra’ila ta kai a gabashin garin Aalamat da ke gundumar Jbeil ya kashe mutum 20 ciki har da yara uku.
Ta kara da cewa an jikkata wasu shida a harin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto domin neman wadanda suka tsira.
Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce mutum 30 da suka hada da kananan yara 13 ne suka mutu a wasu hare-hare biyu da Isra’ila ta kai kan wasu gidaje biyu a arewacin Falasɗinu.
Harin na farko wanda aka kai shi da safiyar Lahadi ya faɗa ne a wani gida da ke Jabalia da ke arewacin Gaza, inda ya kashe aƙalla mutum 25 daga ciki har da yara 13 tare da jikkata sama da mutum 30, in ji hukumar kare farar hular.
Wani harin kuma ya faɗa ne a unguwar Sabra da ke birnin Gaza inda mutum biyar suka rasu, wasu da dama kuma sun ɓata bayan harin.
Hukumar ta kara da cewa, har yanzu akwai fararen hula da dama a karkashin baraguzan ginin.